Kungiyar 'yan tawayen M23 da ke dauke da makamai ta yi gaggawar kwace yankuna da dama a gabashin DRC mai arzikin ma'adinai a wani harin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba adadi mai yawa da muhallansu.
Gwamnatin DRC ta ayyana kungiyar ta M23 a matsayin kungiyar ta'addanci a hukumance, yayin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka sanya ta a matsayin kungiyar 'yan tawaye masu dauke da makamai.
Taron da aka yi a Tanzaniya ya samu halartar shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da takwaransa na Congo Felix Tshisekedi da kuma shugabannin kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC da mambobi 16 na kasashen kudancin Afirka.
Kagame ya bayyana da kansa, yayin da Tshisekedi ya shiga ta bayyana a faifan bidiyo.
A cikin sanarwar karshe, taron ya yi kira ga hafsoshin sojojin na al'ummomin biyu “su gana cikin kwanaki biyar tare da ba da jagoranci na fasaha kan tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba.”
Haka kuma ta bukaci a bude hanyoyin jin kai domin kwashe wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.
A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gwabza fada a tazarar kilomita 60 daga kudancin Kivu babban birnin lardin Bakuvu, kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida da na jami'an tsaro suka shaida wa AFP.
Kungiyar M23 ta kwace babban birnin Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa, a makon da ya gabata, kuma tana kara shiga makwabciyarta Kivu ta Kudu a cikin sabon rikici na tsawon shekaru da dama a yankin.
Dandalin Mu Tattauna