Maharan sun kai farmaki ne a kusa da kauyen Kobe mai tazarar kilomita 30 daga Gao a yankin da kungiyoyin da ke da alaka da kungiyar IS da al-Qaida suka shafe shekaru goma suna tada zaune tsaye a Mali da makwabtanta Burkina Faso da Nijar.
Kimanin gawarwakin mutane 56 ne aka rubuta a asibitin da ke Gao, in ji jami'in, ya kuma kara da cewa akwai kuma wadanda ba a san adadin sojojin da suka jikkata ba.
Sojojin Mali ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba.
Wani mazaunin Gao ya kuma ce an kashe kusan 50 tare da kona motoci. Ana yawan samun munanan hare-hare ta yadda sojoji ke shirya masu rakiya a kullu yaumin, inji mazaunin garin.
Rikicin ya samo asali ne a yankin arewacin kasar Mali bayan samun tawayen 'yan awaren Abzinawa a shekara ta 2012. Tuni dai mayakan suka bazu zuwa wasu kasashe a yankin tsakiyar Sahel da ke fama da talauci a kudancin Sahara.
Hare-haren sun kashe dubban mutane tare da haifar da rikicin jin kai, inda sama da mutane miliyan 3.2 suka rasa matsugunansu ya zuwa watan Janairu, a cewar Kungiyar Kula da Hijira ta Duniya.
Dandalin Mu Tattauna