Yayin da kwararru ke ta hasashen abubuwan da za su biyo bayan taron Davos na tattalin arziki, saboda da halartar taron da Shugaban Donald Trump ya yi, wani kwararre ya ce halartar taron da Trump ya yi sam ba zai sa duniya ta lamunta da manufofin gwamnatin Amurka ta fifita marudun Amurka ba.
Da ya ke yin tsokaci game da wannan taron, wani kwararre kan harkokin tattalin arziki mai suna Malam Yusha’u Aliyu y ace taro ne da ke hankoron karfafa batun inganta rayuwar jama’a da, da tattalin arziki da kuma daidaito ta fuskar kasuwancin duniya. Y ace kamar yadda aka saba yi, kasashen da su ka yi mulkin mallaka don haka su ka san dadin tatsar wasu kasashe su ke yin tasiri a taron.
Da abokin aikinmu Mahmud Lalo ya tambaye shi yadda yak e ganin korafin Shugaban Amurka Donald Trump cewa ana kwarar Amurka, kuma shi zai fi mai da hankali ne kan kare muradun Amurka, sai Aliyu ya ce ita kwarar kanta hawa biyu ce: Da kwarar Amurkawa da kuma kwarar gwamnatin Amurka. Y ace tsarin Amurka na babbar kasa mai bukatar sauran jama’a ne ya janyo abinda shi Trump din ke ganin kamar kwara ce. Ya ce alheri mai saurin samuwa da kuma saurin karewa Trump ke nema wa Amurka da irin wannan manusa ta sa.
Ga cikakkiyar hirar Mahmud Lalo da Malam Yusha’u:
Facebook Forum