Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Yace Kagame Ya Isar Da Fatan Alherinsa Ga Afirka


US President Donald Trump (R) and Rwandan President President Paul Kagame attend a bilateral meeting on the sideline of the annual meeting of the World Economic Forum (WEF) on January 26, 2018 in Davos, eastern Switzerland. / AFP PHOTO / Nicholas Kamm
US President Donald Trump (R) and Rwandan President President Paul Kagame attend a bilateral meeting on the sideline of the annual meeting of the World Economic Forum (WEF) on January 26, 2018 in Davos, eastern Switzerland. / AFP PHOTO / Nicholas Kamm

Shugaban Amurka Donald Trump ya ci gaba da jaddada akidarsa ta muradun Amurka kafin na kowace kasa a duniya, inda ya kara fadar haka a birnin Davos na Switzerland, tare da cewa Paul Kagame na Rwanda yana wa Afirka fatan alheri.

Shugaba Donald Trump na Amurka yau ya gayawa mahalarta taron tattalin azriki na duniya da ake a birnin Davos na Switzerland cewa kullum muradun Amurka ne zai sa a gaba, amma wannan ba wai yana nufin Amurka din ba zata yi aiki tare da sauran kasashen duniya ba.

Trump ya kuma yi hasashen cewa tattalin arzikin Amurka ne zai zama direban jan motar tattalin arzikin sauran kasashen duniya, tare da cewa kullum abinda zai amfani Amurka ne a gabansa kamar yadda ya kamata su ma sauran shugabannin kasashen duniya su ba wa nasu kasashen muhimmanci.

Tun ma kafin yayi jawabin, shugaban na Amurka yayi kokarin yin maslaha da Shugaba Paul Kagame na Rwanda, wanda kuma shine shugaban Kungiyar Kasashen Afirka ta AU.

Musamman ma dangane da kalamin batancin da shi Trump din da ya yiwa kasashen Afirka kwannakin baya, inda ya kira su da kaskantattu kamar ramin shadda.

A haduwar da suka yi, Trump ya nemi Kagame da ya isarwa Afirkawa da kyakyawan fatansa na alheri ga kasashen na Afirka.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG