Hakan na faruwa biyo bayan rarraba makarantun yara da ake, inda ake samun mabiya addini ‘daya zalla a makaranta. Da yake jawabi ga manema labaru a jihar Kaduna jim kadan bayan tashi daga wani taron bita akan yadda za a samar da zaman lafiya a jihar Kaduna.
Mai baiwa gwamnan Kaduna shawara kan harkokin addini Injiya Nmadi Musa, yace gwamnatin jihar zata bude wasu makarantun kwana ta yadda za a dauki ‘dalibai daga kowanne bangare a hada su guri guda, kuma ana tunanin wannan shiri zai taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai a jihar.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar da ta shirya wannan taron bita ga mabiya addinin Krista da Musulmi da ake kira Global Peace Foundation, Sheik Halliru Maraya, yace sun lura cewa da cewa ba a tara mutane a tunatar da su muhimmancin zaman lafiya sai idan wani tashin hankali ya faru.
Taron na tabbatar da samar da zaman lafiya tsakanin al’ummar jihar Kaduna na zuwa ne a dai dai lokacin da ‘dan zaman ‘dar ‘dar, biyo bayan abin da ya faru tsakanin al’ummar Tudun Wada da kuma mabiya masabahar Shi’a a garin Kaduna.
Saurari rahotan Isah Lawal Ikra daga Kaduna.