Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Daraktan Kamfanin Man Najeriya NNPC Ya Kai Ziyara Bauchi


 Babban Daraktan NNPC Dr Maikanti Baru da gwamnan Bauchi, Barrister M.A.Abubakar
Babban Daraktan NNPC Dr Maikanti Baru da gwamnan Bauchi, Barrister M.A.Abubakar

Biyo bayan samun man fetur a yankin tafkin Chadi dake cikin Najaeriya, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sa kamfanin man fetur din kasar NNPC ya kara bincike a jihohin Bauchi da Gombe

Babban Daraktan kamfanin man Najeriya Dr. Maikanti Kachalla Baru ya kai ziyara fadar gwamnan Bauchi inda ya shaidawa gwmnan ya zo ne bisa ga umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari kan binciken neman man fatur a jihar da makwafciyarta, wato Gombe.

Da yake magana da manema labarai yace ziyararsa cika umurnin shugaban kasa ne. Zasu bude aikin binciken karkashin kasa domin tabbatar cewa akwai man fetur a yankin da ya hada da Bauchi da Gombe. Yace zasu yi aiki a yankin da suke kira Gongola Basin da kuma tafkin Chadi. A yankin tafkin Chadi sun samu mai.

Babban Manajan NNPC Dr Maikanti Baru da gwamnan Bauchi A GIDAN GWAMNATI
Babban Manajan NNPC Dr Maikanti Baru da gwamnan Bauchi A GIDAN GWAMNATI

Gwamnan Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana irin taimakon da gwamnatinsa zata bayar domin gudanar da ayyukan. Yace sun yi alkawarin ba NNPC ofishi kyauta da kuma gidajen ma'aikatan da zasu turo jihar.

Sabanin abun da ya faru can baya gwamnan yace tunda yanzu shugaban kasa ne ya tasa keyarsu to ko shakka babu za'a cimma nasara.

Sanata Salisu Matori wanda yayi fice wajen ganin an soma aikin tono man fetur a arewa maso gabas ya dora alhakin jinkirin da aka samu akan rashin kulawar gwamnatocin da suka shude. Yace lokacin da kamfanin Rasha yayi aiki a yankinsu har za'a fara tono sai aka yi watsi da maganar.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG