Kwamitin ya je anguwanni da kauyuka hudu da kuma barikin Giwa na sojoji inda maharan suka kutsa suka kuma saki wadanda ake tsare da su. Kwamitin na karkashin Alhaji Bulama Gobio ya soma ne da ziyartar barikin Giwa inda kwamandan ya nuna farin ciki da karramawar gwamnatin da kuma irin taimakon da kwamitin ya kawo.
Bayan barikin kwamitin ya zagaya zuwa anguwannin Fori da Baltimari da kauyuka hudu da aka kone gidajensu kurmus. Mutanen wadannan kauyukan wasu na kan tsaunuka wasu kuma kamar mata suna zaune cikin tsummokara da yin juyayi. Bugu da kari yawancinsu basu da abun da zasu ci. A daya daga cikin kauyukan mutanen sun ce wanda ya jagoranci wadanda suka kona kauyan daga nan ya fita ya shiga kungiyar Boko Haram.
Wani Malam Bashir Abba wanda yake cikin fararen hulan JTF masu daukan gora da suka fafata da 'yan Boko Haram yayin da suka kai masu hari yace idan Allah Ya yadda harin shi ne na karshe. Ba zasu kara kawo hari a kauyen nasu ba. Yace sun tura masu basu labaran siri kuma suna nan a shirye amma yace ba zai fadi wadanda ke aikin tara labaran ba.
Shugaban karamar hukumar birnin Maiduguri Alhaji Abdulkadiri Rahis yace lokaci yayi da matasan zasu kawo karshen irin wadannan hare-hare cikin ikon Allah
Ga karin bayyani.