Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TARABA: 'Yansanda Sun Kama Wani da Yara 17


Babban sifeton 'yansandan Najeriya Mr. Solomon Arase
Babban sifeton 'yansandan Najeriya Mr. Solomon Arase

Wani da yake ikirarin shi pasto ne mai bishara ya fada hannun 'yansanda da yara goma sha bakwai da yake tafe dasu

Shi paston yana kokarin tetarewa ne da ta bakin kogin Ibi da yaran dake jihar Taraba zuwa jihar Filato kafin jami'an tsaro su tareshi.

Kawo yanzu dai ba'a tantance inda duka yaran suka fito ba amma wasunsu daga yankin Chibok suke. Akwai wasu kuma daga jihohin Yobe da Taraba. Duk su goma sha bakwai din kananan yara ne.

Onarebul Iliyasu Muhammad Ajibo shugaban karamar hukumar Ibi yace tuni aka mika mutumin ga rundunar 'yansandan jihar. Mutumin da aka kama yace shi paston yaran ne to amma jami'an tsaro sunce basu yadda dashi ba. Daga bisani mutumin yace wani sarki na sane da lamarin amma da aka tuntubi sarkin ya musanta maganar.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar Taraba DSP Josaph Kwaji ya tabbatar da lamarin kuma yanzu suna bincike. Kwaji ya gargadi iyaye su sa ido akan shiga da ficen 'ya'yansu saboda masu sacesu suna anfani dasu wajen shirya kai kunar bakin wake.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG