Yayinda yake yiwa masu ruwa da tsaki a harkokin zaben da za'a yi kwamishanan 'yansandan jihar Oyo Alhaji Muhammad Musa Katsina yace yarjejeniyar tana da mahimmanci domin tabbatar da tsaron jama'a.
Kwamishanan ya cigaba da cewa suna da wani nauyi da ya rataya a wuyansu na ganin cewa an tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'umma kafin zabe da lokacin zabe da ma bayan zaben. Suna da aikin gujewa kowace irin tarzoma. Kada a yi wani abun da zai kassara mutuncin mutanen jihar Oyo domin jiha ce dake son zaman lafiya.
Wasu 'yan siyasa da aka zanta dasu sun ce yarjejeniyar ta dace domin a tabbatar da an yi komi lami lafiya. Dukansu sun amince da yarjejeniyar. Suna fata yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa lami lafiya su ma a yi nasu lafiya.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.