Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JIHAR GOMBE TAYI SHEKARU 20 DA KIRKIROWA


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Gwamnatin jihar Gombe tayi shekaru 20 da kirkirowa, a dangane da hakan ne tsohon shugaban kasar Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ke cewa dama wasu jiga-jigan ‘yan siyasar jihar ke cewa

’Gwamna yayi aiki kwarai da gaske, ayyukan gwamnan jihar sunyi kyau sosai, naya ba da ayyukan sa sosai,Yau shekaru 20 da kirkiro jihar , kuma taci gaba amma fatar mu shine ta samu ci gaban da yafi wannan’’.

Shima wani dan siyasar ga abinda yake cewa.

‘’Idan aka duba shekaru 20 da muka yi a matsayin jiha sai kaga mun samu ci gaba a sassa da dama, domin ko wani bangare an taba shim idan ka dubi wasu makwabtan mu da muka samu jihar tare sai kaga Gombe tafi su cigaba sosai, to wannan abin mu godewa ALLAH ne’’.

Shima Faruk Bamusa Sarkin Arewan Gombe ga abinda yake cewa.

‘’Duk wanda zaizo a matsayin shugaba a Gombe a Gaba dole ya zo da abu biyu zuwa ukku, na daya ya zamanto yana tunanen wayayyen kai wanda yake zai kai Gombe a matsayin da Lagos take na biyu duk talakkan Gombe yana cikin talauci, kuma talauci ba abinda mutumin Gombe ya roka wa kansa bane, don haka duk wanda zaizo ya yi tunanen kawo talakkan Gombe cigaba’’.

Shiko shugaban matasan jamiyyar APC Shafiu Idris ga abinda yake cewa.

‘’Munga abubuwa da dama munji dadi munyi murna kamar yadda aka zo akayi abubuwa muka gani da idon mu, Gombe State ta samu ci gaba ta fannoni daban-daban, abinda matasa ya kamata su mayar da hankali akansa shine karatu’’.

Ga Abdulwahab Mohammed da ci gaban Rahoton 3’22

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG