Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya yaba da irin kwazo da hazikancin 'yan Najeriya, a yunkurinta na magance matsaloli da suka addabi kasar ta fuskoki daban daban.
Mr. Kerry ya bayyana haka ne a cikin sakon taya murnar da ya sanyawa hanu a amdadin shugaban Amurka Barack Obama, zuwa ga shugabannin da al'umar Najeriya, a wannan marra ta cika shekaru 56 da samun 'yancin kai.
Mr. Kerry yace bayan ziyararsa ta baya bayan nan da ya kai Najeriya, ya hakikance kasar tana da kwararru wadanda suka dukufa wajen tabbatar da hadin kan kasar ba tareda la'akari da ko wani irin banbanci ba.
Sakataren harkokin wajen na Amurka yace kodashike akwai jan aiki a gaba ta fuskr tattalin arziki, da tsaro, ya hakikance kasar tana da gogaggun mutane da zamu taiamaka wajen ganin kasar ta tsame kanta daga wadannan matsaloli-kama daga 'yan Boko Haram, yaki da cin hanci da rashawa da sauran matsaloli.
Ga karin bayani.