Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tallafin Kudi Na Da Muhimmanci Ga Yaki Da Sauyin Yanayi A Afirka - Akufo-Addo


Taron Afirka kan sauyin yanayi
Taron Afirka kan sauyin yanayi

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yi kira da a cika alkawuran kudi da kasashen da suka ci gaba suka dauka domin taimakawa Afirka wajen yaki da sauyin yanayi.

Shugaban kasar yace, taimakon kudade daga kasashen zai tallafawa kokarin da suke yi na cikin gida. Ya fadi haka ne yayinda yake jawabi wajen taron Afirka kan sauyin yanayi a birnin Nairobi, Kenya.

Babban makasudin taron kolin, na kwanaki uku, shi ne gabatar da kudurin bai daya a taron sauyin yanayi na COP28 da za a gudanar a Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Nuwamba; lalubo dabarun da ke da nufin mayar da Afirka wata babbar cibiyar samar da makamashi mai inganc, tare da neman taimako daga al'ummar duniya don tallafawa wannan gagarumin aiki.

Taron Afirka kan sauyin yanayi
Taron Afirka kan sauyin yanayi

Da yake jawabi a wajen taron, shugaba Akufo-Addo ya jaddada cewa kasashen Afirka na yin nasu bangaren wajen samar da yanayi mai kyau, don haka suna bukatar taimakon kudi na kasa da kasa don kara kaimi ga kokarinsu.

Ya ci gaba da cewa, "Muna iya kokarinmu kan sauyin yanayi a matakin kasa, muna sa ran kuma za a yi ababa da dama a matakin kasa da kasa. Wani babban al'amari da ke damun mu shi ne bukatar daidaita hanyoyin samun kudaden sauyin yanayi na kasa da kasa da zai tallafawa na cikin gida."

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya na 2022 ya kiyasta cewa, Afirka na yin asara daga dala biliyan 7 zuwa dala biliyan 15 a duk shekara, saboda sauyin yanayi. Don taimakawa wajen rage illar sauyin yanayi, kasashen Afirka na bukatar su tara dala biliyan $124 a duk shekara.

Taron Afirka kan sauyin yanayi
Taron Afirka kan sauyin yanayi

Mataimakin Daraktan Bincike a Cibiyar Sauyin Yanayi da Tsaron Abinci, Mohammed Jafaru Dankwabia yace wadanda suka shirya wannan taro sun cacanci yabo, domin samun murya daya ne zai sa kasashen da suke taimakawa karuwar dumamar yanayi su cika alkawarinsu. Yace, Afirka ce ke wahala a sanadiyar dumamar yanayi.

Yana mai cewa, "Wanda ke fitowa daga kasashen Turai, kashi 10 ko 20 cikin dari ne kawai yake fitowa daga Afirka, amma wadanda suke wahala idan ya zo; fari, ambaliya, tsananin zafi da sauransu duka na karewa ne kan Afirka. Domin haka, kasashen Turai da suka yi sanadin haka, lallai su ne ya kamata su na da fansa, kuma idan afirka ta tafi da murya daya, zai sa a samu biyan bukata," in ji Mohammed Jafar.

Taron Afirka kan sauyin yanayi
Taron Afirka kan sauyin yanayi

A cewar masana, hanyar samar da kudade daga kasashen da suka ci gaba, za su taimakawa kasashen Afirka su shawo kan kalubale na musamman da suke fuskanta wajen yaki da sauyin yanayi. Suka ce tallafin ba wai kawai zai taimaka wajen kiyaye muhalli ba har ma da inganta ci gaba mai dorewa da kuma tabbatar da samun daidaito ga kowa a nan gaba.

A Ranar Laraba 6 ga watan Satumba aka kammala taron kwanaki ukun, kuma shugabannin Afirka sun bukaci manyan masu fitar da iskar gas dake dumama yanayi a duniya, da kasashe masu arziki su cika alkawuran da suka dauka na dala biliyan $100bn duk shekara ga kasashe masu tasowa. Haka kuma, suka yi kira ga shugabannin duniya da su marawa shawarar tsarin harajin carbon na duniya, da suka hada da makamashin man fetur, sufurin ruwa da jiragen sama, wanda kuma za a iya karawa da harajin hada-hadar kudi na duniya.

Saurari rahoton Idriss Abdullah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG