Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talauci Da Auren Wuri Cikas Ga Ilimin Mata (Ranar Yara Mata Na Duniya)


Ranar 11, ga watan Oktoba na kowace shekara ranar ce da majalisar dinkin duniya ta ware dominbikin ranar yara mata na duniya wanda majalisar ta kirkiro a shekara ta 2011, inda Majalisar ta samar da wani kudiri da zai duba irin kalubalen da mata yara ke fuskanta a fadin duniya.

Makasudin bikin ranar yara mata na duniya shi ne maida hankula wajen magance kalubalen da yara mata ke fuskanta domin a kyautata masu da suka hada da samun ‘yanci, tsaro, ilimi da kuma kula da lafiya.

Bincike ya bayyana cewa yara mata na kasa iya cimma burinsu masamman a fannin samun cikakken ilimi a sanadiyar talauci da kuma tilasamasu yin aure da wuri sabili da haka ne Majalisar dinkin duniya ta zartar da kudiri na 63, mai lamba 170, a watan Disamba na 2011, domin tabbatar da cewa yara mata sun samu dukkan wata dama da yara maza ke samu a fannonin rayuwa.

A wata cibiyar taimakawa yara mata da suka samu cikas masamman a fannin ilimi a garin Bauchi, wasu daga cikin daliban wannan cibiya sun koka akan yadda ake yiwa yara mata tarnaki da auren wuri dake kuma hanasu ci gaba da ilimi.

Sun kuma kara da kira ga iyaye dasu tabbatar da ganin cewa sun marawa ‘ya’ya mata baya na ganin cewa sun cimma burinsu na samun ilimi, sun kuma bukaci gwamnati da ta kara kula da makarantun yara mata.

Sai dai a halin yanzu gwamnatocin jihohi sun himmatu ta hanyar bullo da shirye shirye domin shawo kan kalubalen da yara mata ke fuskanta dake zama kandagarki a fanin ilimi kamar yadda kwamishinar ilimi na jihar Gombe Hajiya Amina Muhammad, ta tabbatarwa wakilin muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG