Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsirai Da Saiwa Nada Amfani A Jikin Dan-Adam


Maimuna Sani
Maimuna Sani

Magungunan gargajiya nada tasiri wajen kula da lafiyar fatar Dan Adam, idan aka yi amfani dasu abisa kaida bayan an gudanar da bincike akan su.

Hajiya Maimuna Sani. wata mai harkar bada shawara ga lafiyar fata wato Skin image consultancy ne ta bayyana hakan a yayin zantaawa da wakiliyar Dandalinvoa, Baraka Bashir.

Ta ce da fari ta karanci harshen Turanci ne a jami’a, bayan kammalawarta mai gidanta ya bata shawarar bude makaranta, amma hakarsa bata cimma ruwa ba kasancewar ba abinda take buri kenan ba, ko da yake ta ce tun kafin nan ta so ta karanci aikin jarida amma sai ya kasance ba a nan Gizo yake sakarba.

Maimuna ta ce ta tafi kasar Spain wato Andalus inda ta kwari a karkar fata, amma ba’a likitance ba illar kawar na iya lura da wasu lallurorin da fata kan yin fama da su kamar kuraje ko wasu abubuwa da abinda da ake ci na nauin abinci ke haifar da shi.

Ta kara da cewa bincike ya nuna cewar nahiyar Afrika na da tsirai da saiwa da amfani da su na da matukar muhimmanci a fatar jikin dan Adam, wanda kamfaninta ke saraffawa domin dacewa da fatar ‘yan Afrika.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:19 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG