A jiya Lahadi ne aka fara gasar tseren motoci masu amfani da hasken rana, wanda ake gudanarwa a kasar Australia. Kimanin motoci 42 suke cikin wannan gasar. Gasar da akayima take ‘Australia Tropical North’ gasace da motoci zasu zagaye kasar ta Australia.
Za’a fara gasar daga garin Darwin dake arewacin kasar zuwa birnin Adelaide dake kudanci kasar, mai tafiyar kimanin kilomita dubu uku 3,000, kwatankwacin tafiya daga birnin Maiduguri zuwa Lagos. Tafiyar dai, idan aka kwatanta ta da sauran tafiyoyi, za’a ga cewar tafiyace da zata iya kwashe mako guda anayi.
Amma tafiyar da motocin tsare ne za suyi da suke gudu cikin sauri, suna tafiya da takai kimanin kilomita 90-100 a cikin awa daya. Motar da aka taba samu a tarihi tayi matsiyacin gudu itace wata mota kirar jami’ar Tokai dake kasar Japan a shekarar 2009.
Motocin basa amfani da wani nau’in mai don tafiya, suna dogaro da hasken rana dari bisa dari 100%, duk motocin wannan shekarar sun fita da ban da na sauran shekaru, kuma akwai alamun zamuyi nasara a wannan gasar, inji manajan wani kamfani Mr. Sarah Benninkbolt.
Wannan shine karo na 30 da ake gudanar da gasar tseren motoci masu amfani da hasken rana, akwai kimanin kasashe 40 da suka shiga cikin gasar, kasashen sun hada da kasar Amurka, Japan, Germany, Chile, Netherlands, Birtaniya, Malaysia, Belgium, Sweden, Iran, Korea ta kudu, India, Hong Kong, Afrika ta Kudu, Poland, Thailand, Turkey, Canada, Taiwan da Australia.
A cewar ministan birni da al’adu Mrs. Lauren Moss, tace gwamnatin kasar Australia, a shirye take ta bada lada ga wanda ya lashe gasar, na kudi da suka kai kimanin dalar Amurka $250,000, da zummar kawo karshen gurbatar yanayi nan da shekarar 2030.
Facebook Forum