Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, dake kasar Ingila, tana daf da cimma yarjejeniya tsakaninta da dan wasan tsakiyarta Marouane Fellaini, kan batun sabunta kwangilarsa a kungiyar.
Fellaini, mai shekaru 29, da haihuwa an haifeshi ne a kasar Belgium, a wani gari mai suna Etterbeek Brussia, a ranar 2, ga watan Nuwamba 1987.
Dan wasan ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Anderlecht, na matasa dake kasar ta Belgium, daga shekara 1994 - 1997,
Ya kuma buga wasannin a kungiyoyin kwallon kafa da dama na matasa, inda daga bisani ya Koma kungiyar Standard Leige duk a kasar ta Belgium, a 2004 har zuwa 2006. ya samu nasarar shiga tawagar babbar kungiyar ta Standard, 2006 zuwa 2008 sai ya bar kasar Belgium, zuwa kungiyar kwallon kafa ta Everton, na kasar Ingila a 2008 zuwa 2013.
Dan wasan ya dawo kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ne a shekara ta 2013, daga Everton, inda Manchester ta bashi riga mai lamba 27.
Fellaini ya samu damar shiga wasanni a kungiyar ta Manchester United, sau 95 yayi nasarar jefa kwallaye 11 a raga a wasannin daban daban.
Saboda irin kokarin da dan wasan yakeyi a kungiyar ta Manchester United shi yasa mai horas da kungiyar Jose Mourinho, ya bukaci dan wasan da sake tsawaita zamansa a kungiyar, ta Manchester United.
Facebook Forum