Mahaifin marigayi Flt. Lt. Alfred Olufade, matukin jirgin saman soji da ya yi hatsari a Kaduna George Olufade, ya ce addu’ar ‘yan kasa ya ke bukata domin ita ce kawai za ta iya rike shi, bayan rasa da daya tilo da ya ke shi.
Hatarin jirgin saman ne ya kuma yi sanadiyar mutuwar babban hafsan sojin Najeriya, Lt. Gen. Ibrahim Attahiru, da wasu manya da kananan hafsoshi 10.
George Olufade, ya koka da mummunan halin da jiragen sojin kasar ke ciki tare da yin kira ga hukumomi da su rika duba lafiyar jiragen da yin gyare-gyare lokaci zuwa lokaci domin kawar da aukuwar hatsari a nan gaba.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, marigayi Alfred Olufade, ya yi aure ne watanni uku da suka gabata cikin murna, wanda hakan ya jefa matarsa da sauran ‘yan uwansa cikin matsanancin damuwa.
Mahaifin sa ya bayyana cewa, mutuwar dan sa ta sanya shi cikin bakin ciki matuka ya na mai cewa yana bukatar addu’a don cin wannan jarabawa na rashin dan sa.
Karin bayani akan: Alfred Olufade, Ibrahim Attahiru, Kaduna, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Olufade ya ce marigayin dan sa ya kasance mai hankali, karamci, mai kaskantar da kai, da sadaukarwa ga aikinsa da ya zaba bayan dawowa daga makarantar koyar addini.
Ya kara da cewa dan nasa, da ne na musamman kuma shi kadai ne jami’in sojin sama a jiharsu wanda ya kamalla karatu ya da mafi karancin shekaru a shekarar da suka kammala karatu, ya kuma tallafa masa daga farko zuwa karshen karatunsa a makarantar sojin sama a matsayin mahaifinsa tun da ya bayyana sha’awar zama matukin jirgin sama.