Rahotannin daga Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya na cewa ana can ana kintsawa a jana’izar da za a yi wa babban hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.
Attahiru ya rasu a ranar Juma’a tare da wasu sojoji 10 cikin har da janar-janar, a lokacin da jirginsu ya fadi a kusa da filin tashin jirage na kasa da kasa da ke Kaduna.
Bayanai sun yi nuni da cewa za a gudanar da jana’izar ce da misalin karfe dayan a makarbartar dakarun kasar da ke Abuja, bayan an masa sallah a babban Masallaci na kasa da ke birnin.
Jana’izar har ila yau ta hada har da wasu sojoji biyar daga cikin sojojin da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin, wadanda Musulmai ne.
Karin bayani akan: Janar Ibrahim Attahiru, Boko Haram, sojoji, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Daga cikinsu akwai mai tsaron lafiyar Attahiru, Manjo Lawal Hayat.
Wata sanarwa da kakakin sojan Najeriya Brig. Gen. Mohammed Yerima ya fitar, ta ce za a gudanar da jana’izar wasu daga cikin wadanda suka rasu a hatsarin wadanda mabiya addinin Kirista a babbar Mujami’ar Abuja.
Hatsarin ya auku ne yayin da tawagar sojojin ke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce tana kan bincike don gano musabbabin wannan hatsari, wanda shi ne na kusan uku da ya rutsa da jiragen sojin Najeriya a wannan shekara.
A watan Fabrairun bana, wani jirgin sojin saman kasar ya fadi a yankin Abuja, babban birnin tarayyar kasar dauke da sojoji bakwai – dukkaninsu sun mutu.
Sannan a watan Afrilu, wani jirgin saman sojin Najeriya da ke kai wa dakarun kasa dauki a yaki da mayakan Boko Haram, ya yi batan dabo.
Boko Haram ta yi ikirarin ita ta kakkabo jirgin wanda ke dauke da matuka biyu, amma rundunar sojin Najeriyar ta musanta ikirarin kungiyar.
A ranar 10 ga watan Agustan shekarar 1966 aka haifi Janar Attahiru a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A watan Janairu aka nada shi a matsayin babban hafsan sojin kasar.
Bayanai sun yi nuni da cewa, Attahiru ya taka rawar gani a yakin da dakarun Najeriya ke yi da mayakan Boko Haram, ya kuma rike manyan mukamai daba-daban a rundunar sojin kasar.