Takaddamar mallakar gidaje, filaye da gine-gine a biranen Najeriya abu ne da ke neman zama ruwan dare, walau a tsakanin daidaikun mutane, hukumomin gwamnati da ‘yan kasuwa ko kamfanoni masu zaman kansu.
Kano na daya daga cikin birane a Najeriya da ke fama da irin wadannan matsaloli.
Ko da yake a shekarun baya, wannan matsala ta fi wakana ne a tsakanin daidaikun mutane, musamman attajirai, inda kusan kowace kotu a Kano ba ta rasa shari’un da suka shafi gonaki, fulotai, gidaje ko rumfar kasuwa.
Sai dai a shekarun baya-bayan nan lamarin na rikidewa ya koma tsakanin hukumomin gwamnati da daidaikun mutane ko kuma tsakanin ‘yan kasuwa, kamar yadda ya ke faruwa tsakanin hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, wadda ke binciken ikirarin da wani dan kasuwa ke yi na cewa, ya sayi filin gandun Sarki na Dorayi karama da ke daura da Jami’ar Bayero mai fadin Hecta 22 kan kudi naira miliyan 700.
Barrister Muhuyi Magaji, shugaban hukumar rashawa ta jihar Kano, ya ce ya ga takardar da sarki Waziri ya ce ya saida wurin akan naira miliyan 200, amma a cikin takardar kuma an ce an saida na masarauta na magada a kan naira miliyan 575 kuma na masarautar ya linka na magada. Don haka dole ne hukumar ta yi bincike.
Sai dai tuni wannan dan kasuwa Alhaji Yusuf Aliyu Shu’aibu ya garzaya kotu don neman dakatar da binciken hukumar. Lauyan sa Barrister Ahmad Sani Bawa ya bayyana cewa sun je kutu ne don kotu ta yi amfani da karfinta ta dakatar da wanda ke amfani da jami’an da ke karkashin sa don neman keta haddin bawan Allah akan hakkinsa.
Ko a shekara ta 2019 hukumar yaki da rashawa ta Kano ta gudanar da makamancin wannan bincike akan masarautar Kano kan yadda aka yi cinikayyar fulotai da gidajen da aka gina a gandun Sarki na Darmanawa.
Kazalika irin wannan takaddama ce ke wakanan tsakanin mazauna unguwar Darmanawa layout da majalisar masarautar Kano kan batun filin Idi.
A hannu guda kuma, akwai makamanciyar wannan takaddama tsakanin majalisar gidan zakka mai zaman kanta da gwamnatin jihar Kano.
Malam Kabiru Sa’idu Sufi mai sharhi ne kan lamuran yau da kullum, ya bayyana wasu daga cikin dalilan da suka janyo irin wadannan rikice-rikice, inda ya ce a baya akwai wasu kungiyoyi da hukumomi da suka sayi filaye da niyar zuba jari amma daga baya aka sami sauye-sauye a hukumomin ko kungiyoyin sai ya kasance an sami canjin manufofi.
Saurari karin bayani cikin Sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari