Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Wani Matashi Da Kashe Matarsa Akan Kunu


Lawali Danladi, wanda ake zargin ya kashe matarsa.
Lawali Danladi, wanda ake zargin ya kashe matarsa.

‘Yan sanda a jihar Neja sun ce suna bincike kan wani matashi dan kimanin shekara 20 mai suna Lawali Danladi da ake zargin ya kashe matarsa.

Lamarin ya faru ne a kauyen Kadaura da ke yankin Yakila a karamar Hukumar Rafi ta jihar Nejar a cewar ‘yan sandan, wadanda suka gabatar da matashin da ake zargi ga manema labarai.

Wanda ake zargin dai ya ce sun yi fada da matar shi ne akan kunun da ta dama, wanda ya dauka ya baiwa yara.

“Da na sha ludayi biyu, sai na ba yaran kunun, sai ta taso da fada tana zage-zage, har da hadawa da mahaifana, daga nan, sai ni kuma na tashi da zuciya, na dan mare ta sau biyu, na tashi na bar ta.”

Karin bayani akan: Lawali Danladi, jihar Neja, Nigeria, da Najeriya.

A cewar Danladi mahaifinsa ne ya tarar da shi ya fada masa cewa ana zarginsa da ya kashe matarsa saboda fada da suka yi.

“Babana ya zo ya ce, an ce ka yi fada da matarka, an kuma ce fadan da kuka yi shi ne sanadiyyar rasuwarta.” Danladi ya fadawa manema labarai yadda ya samu labarin mutuwar matar tasa.

Kwamishinan ‘yan sandan Nejan Adamu Usman ya ce da sun kammala bincika za su kai shi kotu domin fuskantar hukunci.

Wannan lamari ya faru ne kasa da mako guda, bayan da wata mata ta kashe kishiyarta a jihar ta Neja, inda a ranar Larabar da ta gabata aka gurfanar da ita a gaban kotu, bayan da ‘yan sanda suka kammala bincikensu.

Saurari takaitaccen rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:19 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG