Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Yakin Syria Na Iya Rikide wa Ya Koma Na Duniya?


Wannan shi ne sakamakon hare-haren da Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai kan wata cibiyar bincike ta kimiyya a birnin Damascus na Syria
Wannan shi ne sakamakon hare-haren da Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai kan wata cibiyar bincike ta kimiyya a birnin Damascus na Syria

Masana a sassan duniya, na fadin albarkacin bakinsu, dangane da abin da ka iya biyo bayan hare-haren martani da Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai a Syria.

Tun gabanin Amurka ta jagoranci hare-haren da aka kai wa Syria a daren jiya, masu fashin baki ke nuna fargabar kada lamarin ya rincabe ya kai ga yakin Duniya na uku.

Hasali ma, Rasha wacce ke goyon bayan gwamnatin Syria, ta yi gargadi a farko cewa, za ta dakile duk wani hari da Amurka za ta kai akan Syrian.

Hakan ya tunzura shugaba Donald Trump a tsakiyar makon nan ya ce, Rasha ta zauna cikin shiri domin "hare-harensu na tafe."

Wannan cece-ku-ce, ya biyo bayan harin makami mai guba da ake zargi gwamnatin Bashar al- Assad da amfani da shi a kan ‘yan kasarsa, lamarin da Amurka ta ce sai ta dauki matakin soji akai.

Akalla mutane 40 aka yi kiyasin sun mutum a harin na makami mai guba wanda rahotannin suka ce an kai shi a yankin Douma, da ke wajen Damascus babban Birnin kasar ta Syria.

Abin Da Masana Ke Hange

To sai dai Dr. Hafiz Muhammad Sa’id, shugaban Cibiyar Haidar Center a Najeriya, wanda masani ne kan siyasar yankin Gabas ta Tsakiya, ya ce, zai yi wuya, yakin na Syria ya rikide ya zama na Duniya.

“Wannan ba hari ne na gama-gari ba, ko yau za mu ga Firayi Ministar Birtaniya, ta ce harin sun kai ne domin ladabtar da shi Assad, ba wai sun kai hari ne ba domin a kawar da Assad.” Inji Dr. Sa’id.

Ya kara da cewa idan yakin suke so su (Amurka da kawayenta) yi, wannan yana nufin, hare-harensu zai hada da sojojin Rasha da na Iran da na Hezbolla, idan lamarin ya yi zafi, wadannan su ma za su iya kai hari akan Isra’ila, amma ba ma tunanin abin zai kai ga haka.”

Shi ma Benham Ben Talebu, jami’i a Gidauniyar Kare Mulkin Dimokradiyya da ke nan Amurka, ya bi ra’ayin Dr. Sa’id.

“Ina ganin, Amurka na so ne ta mayar da hakalinta kan makamai msu guba, ba wai ta saka kanta cikin sarkakiyar siyasa da yaki na soji ba, wannan wani martani ne ga abotar da Assad yake yi da Rasha da kuma Iran ba.”

Saurari abin da Dr. Hafiz Muhammad Sa'id ya ce:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:28 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG