Biyo bayan mutuwar Falasdinawa 29 a wata zangar zangar da suka yi arangama da yan sandan Isra’ila a kwanan nan, kotun kasa da kasa mai binciken manyan laifuka ta ICC tayi kira ga kawo karshen zubda jinin a zirin Gaza.
Fatou Bensouda tace dama ofishinta yana gudanar da wasu bincike da farko a yankin Falasdinawar, don haka tana sa ido sosai a kan yankin.
Tace duk wani laifi da ake zargin aikatawa a yanayin da ake ciki a Falasdinu, akwai yiwuwar gabatar da kara ga ofishinta ya tantance.
Rahotannin sun nuna ana binciken Isra’ila a kan mutuwar Falasdinawa 29 yayin wata zanga zangar kwanaki 10 da kuma arangamar da aka samu a kan iyakar zirin Gaza.
Isra’ila ba mamban kotun ba ce kuma ta musunta cewa Falasdinu ba kasa ba ce, don haka bata da hurumin shiga wannan kotun.
Kotun ICC itace kotun duniya guda daya mai cin gashin kanta dake binciken manyan laifukan yaki. An kafata ne a shekarar 2002domin tayi binciken kisar kare dangi,da laifukan yaki da kuma laifukan da aka yiwa bil adama.
Facebook Forum