Kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Sunday Oliseh ya bayyana cewa kungiyar ‘yan wasan Najeriyar wato Super Eagles na samun ci gaba a karkashin jagorancinsa, ya fadi haka ne a bitar shugabancinsa wanda aka kwashe watannin biyar zuwa yanzu.
Tsohon dan wasan tsakiyar filin na Super Eagles yace, aiki ne ja a ce ka zama mai horar da ‘yan wasan kasar da take da yawan al’umma sama da Miliyan Dari da Saba’in, sannan kasa mai cike da masu tsokaci kan tamaula, da kuma masu horar da ‘yan wasan kwallon kafa.
Kungiyar ta buga wasnni 8, ta ci wasanni 4, ta yi kunnen doki 3, ta rasa wasa 1. Sannan ta ci kwallaye 9 tare da sadaukar da guda 2 a karkashin Oliseh.
Yace kungiyar yan wasan suna da sabbin jinni irin su Moses Simon, Sylvester Igboun, Chima Akas, Paul Onobie, Shehu Abdullahi, Carl Ikeme, Odion Ighalo, Austin Obaroakpo da makamansu. Wadanda sababbin ne amma sun zama taurari a tawagar ‘yan wasan na Super Eagles.
A karshe Oliseh ya godewa masoyan Kungiyar tamaular da cewa suna nuna musu goyon bayan da ke kara mujsu kwarin gwiwa sannan suna maraba da suka mai ma’ana don sake ciyar da kungiyar kwallon gaba.