Wani bafalastine mutumin kasar Israel, ya tsinci wani bangaren siminti ko “Tiles” a turance, na farfajiyar fadar wani sarki da yayi zamani da wasu daga cikin annabawa. Shi dai mutumin mazauni anguwar masu kudi ne a kasar. Wannan bangare na gidan sarautar wancan zamanin, wani abun tarihi ne da za’a yi bukin bayyanar da wannan abun mamakin a daukacin kasar a ranar Litinin mai zuwa.
Masana tarihi sun bayyanar da wannan bangaren ginin, da cewar yana da kimanin shekaru dubu daya da dari bakwai 1,700. Dama dai antaba samun irin wannan abun da yayi kama da na mutane da a shekarar 1990. Yanzu haka dai ana shirye-shiryen maida wannan wajen wani gidan tarihi, kuma za’a saka wadannan abubuwan tarihin cikin gidan tarihi da yafi kowane a duniya.
Zanen dake jikin wannan bangaren gidan, yana nuni da cewar wadanda sukayi wadannan zane, mutane ne masu matukar hazaka, kuma alamu sun nuna cewar da hannu sukayi zanen, ba irin na wannan zamanin bane da ake yi da ingina.