Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yadda Za'ayi Mutun Yayi Amfani Da Ruwan Miliyan A Wata?


Ruwa
Ruwa

Kuskure wajen aiwatar da wasu abubuwa a rayuwa bangare ne na jikin dan’adam. A ko ina ana iya samun mutun da aiwatar da wasu kura-kurai, ko kuma ana iya samun abubuwa da mutane suka kera da aiwatar da wasu kura-kurai, kamar kwamfuta, wasu ingina don wasu aikace-aikace.

Wasu mazauna wata anguwa a jihar Verginia ta kasar Amurka, sun koka matuka dangane da bill na ruwa da aka kawo musu a cikin wata daya. Daya daga cikin mutanen ya bayyanar da cewar an kawo mishi bill na dallar dubu biyar $5000 a wata daya, dai-dai da naira milliyan daya da dubu dari daya 1,100,000 wasu kuma an kawo musu na $1,500 wanda baki daya abun da suke biya a baya can bai wuce $75 ko kusa da haka a wata ba.

Don haka suna bukatar gwamnatin karamar hukuma ta binciki al’amarin, a dai ta bakin shugaban karamar hukumar, yace kodai ace mashinan dake bayyana yawan ruwan da mutun yayi amfani, da su a wata sune suka lalace, ko kuma ma’aikata ne basu yin aikin su yadda ya kamata. Kuma zasu dauki kwararan matakai wajen gyara matsalar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG