Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wane Shugaban Kasar Amurka Yafi Kudi?


Shugaban Amurka Da suka fi kusi
Shugaban Amurka Da suka fi kusi

An bayyanar da shuwagabannin kasar Amurka, da sukafi kudi, kodai a lokacin mulkin su da bayan mulki. Shugaban kasa John F. Kennedy, shine shugaba da yafi kowannen shugaban kasar Amurka kudi. Duk dai da cewar bashi ne mai kudin ba, mahaifin shine mai kudi a wannan lokacin, don mahaifin shi dan kasuwa ne, da kuma harkar siye da siyar da hannun jari kana kuma yana sayar da giya, duk dai da cewar siyar da giya a wancan lokacin haramun ne. Amma dai yana da karfin juya dukiyar uban a wancan lokacin. An bayyanar da kudin shi da suka kai kimanin dala billiyan daya $1B dai-dai da naira billiyan dubu dari biyu da ashirin 220,000,000,000. A wancan lokacin.

Sai wanda ya zama na biyu shine George Washington, shima dai yafito daga gidan masu hali, iyayen shi sun samu kudin sune ta hanyar dillancin filaye a jihar Verginia, an kiyasta kudin shi a wancan lokacin da suka kai dalla milliyan dari biyar da ashirin da biyar $525M dai-dai da naira billiyan dubu dari da sha biyar da milliyan dari biyar 115,500,000,000.

Sai na uku shine Thomas Jefferson, shima dai kamar sauran masu kudi dan kasuwa ne, ya samu kudin shine ta harkar saye da sayar da filaye da gidaje, a wancan zamanin ya gina wasu rukunin gidaje da ake kira Monticello, wanda har a wannan zamanin, suna daga cikin gidaje masu tsari na zamani. Kudin shi sun kai dalla milliyan dari biyu da sha biyu $212 dai-dai da naira billiyan dubu arba’in da shida da milliyan dari shidda da arba’in 46,640,000,000.

Zamu cigaba da kawo muku sauran wadanda sukafi kudi, ku cigaba da ziyartar mu a shafin mu na Dandalinvoafacebook.com

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG