Kundin, wanda aka ce shi ne mafi girma da aka taba bankadowa a tarihin bil'adama, na nuna yadda wasu 'yan siyasa kimanin 143, ciki har da Shugabannin kasashe 12, su ka yi ta amfani da wasu dabarun kasashen ketare na kauce ma haraji da ladabtarwa.
Cikin 'yan Afirka da aka ambata a kudin har da wani dan'uwan Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma, da wata 'yar'uwar Shugaban Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo Joseph Kabila, da daurarren tsohon gwamnan jihar Delta mai arzikin man fetur a Najeriya, da Ministan Mai na Angola, kasa ta biyu a arzikin man fetur a Afirka bayan Najeriya.
Stanley Achonu, jami'in gudanarwar Budgit, wata kungiyar sa-kai da kan fassara kasafin kudin gwamnatin Tarayyar Najeriya dalla-dalla ga talakawa, ya ce kodayake ba laifi ba ne amfani da wata kafar kasar waje, kwarmato wannan kudin ya dada jaddada abin da 'yan Afirka su ka dade da sani game da wasu daga cikin Shugabanninsu, cewa su kan yi amfani da asusun ajiyar banki na kasashen waje don boye kudaden jama'a da su ka sace.
James Ibori, wanda ya yi gwamnan jahar Delta mai arzikin mai daga 1999 zuwa 2007, ya amsa laifinsa a wata kotun London a 2012 game da laifukan almundahana da bad da sawun kudaden haram. Ibori ya amsa cewa ya yi amfani da matsayinsa na gwamna wajen karkatar da dala miliyan 75 daga Najeriya, ta wajen fakewa da wasu kamfanonin kasashen waje, kodayake hukumomi sun ce kudaden da ya karkatar a zahiri sun ma zarce dala miliyan 250. Tuni aka yanke masa hukuncin dauri shekaru 13.
Wannan kundin ya kuma ambaci, Alaa Mubarak, wani dan tsohon Shugaban kasar Masar Hosni Mubarak da Ian Stuart Kirby, Shugaban Kotun Daukaka Kara Ta Botswana da kuma tsohon Jakadan Zambiya a Amurka, Attan Shansonga.