Taron da suka yi a karkashin shugabancin ministan tsaron kasar Kamaru ya tattaro hafsoshin sojoji daga Chadi, Najeriya, Nijar, Kamaru da Benin.
Bara ne cikin watan Janairu kasashen suka kafa rundunar sojojin hadin kai domin yaki da kungiyar Boko Haram a kasashensu. Hadakar rundunar sojojin ta fara aiki ne gadan gadan a watan Nuwamban 2015.
Tunda sojojin suka fara yaki da Boko Haram suna ta samun nasarori a kai a kai akan 'yan kungiyar ta'addan ta Boko Haram.
A wannan taron da suka yi sun tsara sabbin matakai.
Babban Sakataren Hukumar Raya Tafkin Chadi Sanusi Imrana Abdullahi ya kira sojojin da suka kara mayar da hankali saboda samun nasara.
Shi ma ministan tsaron kasar Kamaru bayan ya yabawa sojojin ya sake jaddada manufar shugaban kasar Kamaru Paul Biya wanda ya yi alkawari bada duk taimakon da ya kamata ga rundunar hadin gwuiwar domin su cigaba da yaki da 'yan ta'adan Boko Haram.
Dangane da batun jagoranci a faggen faman mataimakin shugaban sojojin kasar Benin Lauren Amuso yace kasarsa ta yaba da yadda ake gudanar da jagorancin yakin na hadin gwuiwan. Yace yaki da ta'adanci musamman na Boko Haram kasa guda ba zata iya gudanar da shi ba har ta cimma nasara. Amma da hadin gwuiwa za'a iya ganin bayansu.
Kawo yanzu sojojin hadin gwuiwa dubu takwas ne ke yaki da 'yan Boko Haram. Mahalarta taron sun ce ya kamata a yi da kaske domin a kawar da 'yan ta'adan daga doron kasa.
Ga karin bayani.