Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya da Nijar Sun Rattaba Hannu a Wata Yarjejeniyar Habbaka Tattalin Arziki


Yarjejeniyar dai na zaman wani kokari da Najeriya da Janhuriyar Nijar ke yi na kara dankon zumunci da kuma bunkasa mu'amullar kasuwanci tsakanin kasashen.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaran aikinsa na Janhuriyar Nijar Mouhammadou Issoufou, sun sanyawa wata yarjejeniya hannu a birnin tarayya Abuja, da zata kai ga shigo da danyen mai daga Janhuriyar Nijar, daga na a tace shi a Najeriya.

Wannan babban aikin na kafa matatar mai dai a garin Mashi dake jihar Katsina za a yi shi, ana sa ran zai samarwa dubban ‘yan Najeriya da Nijar ayyukan yi, ganin irin yawan kudaden da za a kashe da kuma muhimmancin kasuwancin man fetur wanda zai bazu a duk sassan Najeriya.

A wurin rattaba hannun, shugaba Mohammadu Buhari ya ce yana sa ran nan ba da jimawa ba za a samu irin wannan gurbataccen man a wasu yankuna a arewacin Najeriya.

Malam Ibrahim Zakari Talba, shine shugaban kamfanin da ake kira Black oil energy, kamfanin da ya tattara kwararru da masana daga kasashen ketare wajen saka jari, wanda zai kai wannan zunzurutun kudin da suka haura naira miliyan dubu dari 7 domin tabbatar da cewa wannan babar matatar ta fara aiki daga shekara 3 zuwa 5.

Talba ya kuma ce an basu izinin sayen mai daga Nijar yanzu, amma gwamnatocin kasashen biyu sun kafa wasu kwamiti guda 2 da zasu yi bincike su kuma yi nazarin aikin na tsawon watanni 3 zuwa 4.

Malam Garba Shehu, kakakin fadar shugaban Najeriya ya jaddada alfanun da kasashen biyu zasu samu idan wannan aikin ya kammalu.

Ga karin bayani cikin sauti a cikin rahoton Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG