Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Bada Riga Kafin Zazzabin Cizon Sauro a Nijar


Hoton Sauro
Hoton Sauro

A jamhuriyar Nijar, hukumomin kiwon lafiya sun kaddamar da shelar riga kafin zazabin cizon sauro ga yara daga shekaru uku zuwa biyar a birane da karkara.

Sanin kowa ne zazabin cizon sauro na daya daga cikin cututtukan dake haddasa asarar rayukan kanannan yara. Yanzu haka ma'aikatan asibiti ne a Jamhuriyar ta Nijar ke bin gida-gida suna rarraba maganin.

Maganin da ake kira CPS a takaice, wanda a cewar wata jami'ar kiwon lafiya Hajiya Yaha a asibitin PMI Stade dake Damagaram, ta ce bada maganin yayi tasiri a yadda suka lura, yanzu babu yawaitar cutar tunda aka fara amfani da maganin, su ma iyaye sun himmatu wajen kai yaransu asibiti don karbar maganin.

Hajiya Yahar ta kuma bayana irin sauyin adadin mutanen da ke shigowa da zazzabin cizon sauro inda ta ce yanzu a sati sukan samu mutane 20 zuwa 25 sabanin a da da ake samun har mutane akalla 700 dauke da zazzabin cizon sauro a cikin sati daya kawai. Ga cikakken rahoton cikin sauti daga kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG