Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sun Gwammace Daukar Masu Basu Abinda Suke So Maimakon Kwararru: Gloria Moses


Shahararriyar ‘yar wasan gina jikin nan ‘yar asalin Najeriya mai zama a kasar Amurka Gloria Moses ta ce ta koma kasar Amurka a karshen shekarar data gabata bayan kin amincewa da yunkurin kwana da ita da babban mai horas da ‘yan wasan kungiyar tasu yayi kafin ya yarda ta wakilci kasar a wasannin.

Gloria ta bayyana cewa sau tari babban kocin ya nemi ya kwana da ita amma data ki amincewa sai aka cireta daga sansanin horas da ‘yan wasan a shekarar 2013,

inda aka fada mata cewar anga alamun ta yi amfani da haramtattun kwayoyin kara kuzari a sakamakon gwajin da aka yi mata yayinda suke shirshiyen tafiya wasannin a kasar Malaysia.

‘yar wasan kamar yadda mujallar punch, ta wallafa ta bayyana cewa Gloria ta ce, “sun ce sakamakon gwajin da suka yi mani ya nuna cewa ina amfani da haramtattun kwayoyin kara kuzari a gwajin da suka yi mani a shekarar 2013, da basu hana ni kasancewa a sansanin horas da ‘yan wasan ba, da kuma saka ni cikin halin kakanika yi ba da yanzu na zama daya daga cikin zaratan ‘yan wasan da suka halarci wasannin Olympic”.

Ta kara da cewa, “na bukaci a bani sakamakon gwajin tunda ance an ga kwayoyin kara kuzari a sakamakon gwajin da aka yi mani, kuma ya kamata a aikawa jiha ta, jihar Bayelsa kwafi guda, amma har yanzu shiru kake ji, babu wanda yace mani komi, dalilin komawata kasar Amurka kenan”.

Daga karshe Gloria ta bayyana cewa masu horas da ‘yan mata a Najieriya, sun gwammace su aje kwararrun ‘yan wasa a gefe guda su dauki wadanda ke basu abinda suke bukata. Ta kuma bayyana cewa irin mawuyacin halin da ta sami kanta ciki ya kusa sa ta hallaka kanta a Legas.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG