Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talakawa Zasu Kashe Sama Da Naira Billiyan 62, Wajen Bukin Rantsar Da Shugaba!


Zabbaben Shugaban Kasar Amurka Donald J. Trump
Zabbaben Shugaban Kasar Amurka Donald J. Trump

Hukumomi na cigaba da shirye-shirye, don gudanar da bukin rantsar da zabben shugaban kasar Amurka, na arba’in da biyar, wanda zai dauki kimanin mako daya ana gabatar da bukukuwan. Zababben shugaban kasar Donald J. Trump, wanda yake dan kasuwa, ya zama mutun na farko da zai shiga fadar, ba tare da aiki a cikin gwamnati ba a baya.

An dai kiyasta wannan bukin na rantsar da shugaban, zai ci kudi da suka kai kimanin dallar Amurka milliyan dari biyu $200M, wanda yayi dai-dai da naira billiyan sittin da daya. Duk dai da cewar, wannan bashi ne takamaiman abun da za’a kashe ba.

Ana iya samun kari ko ragi, hakan ya danganta da yanayin da aka tashi da shi a ranar rantsarwar. Tsabar kudin zasu fito ne daga aljihun gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, kana da na kananan hukumomi. A takaice ana iya cewa talakawan kasar su zasu dauki wannan dawainiyar.

A bangaren tsaro kuwa, jami’an tsaro sun kwashe tsawon shekara daya, suna shiri akan wannan ranar, wanda yanzu haka akwai kimanin sama da jami’an tsaro dubu ashirin da takwas, a babban birnin tarayya, wanda aka dauko su daga wasu jihohin, don samar da tsaro a lokacin gudanar da bukin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG