Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sultan Ya Kira Malaman Jami'o'i Su Janye Yajin Aiki


Daya daga cikin jami'o'in dake rufe a Najeriya
Daya daga cikin jami'o'in dake rufe a Najeriya

Yayin da yake bude baki da kungiyar 'yan jarida da suka kaimasa gaisuwa Sultan ya kira malaman jami'o'i su janye yajin aiki su rungumi tattaunawa

Maimartaba Sarkin Musulmi Mohammad Sa'ad Abubakar yayin da ya karbi bakuncin 'yan jarida da suka kaimasa ziyarar bude baki ya nuna takaicinsa dangane da yawan yajin aiki da malaman jami'o'i ke yi a Najeriya.

Sultan ya ce yajin aiki da malaman ke yi a Najeriya kadai ake irin wannan yajin aikin. Abun takaici kuma shine yajin aikin 'ya'yan talaka kadai yake shafa da kuma gurbata harakar ilimi a kasar.

Ya ce 'ya'yan masu hannu da shuni suna zuwa jami'o'i ko a waje ko masu zaman kansu su kammala karatunsu cikin shekaru hudu yayin da 'ya'yan talaka na kwashe wajen shekaru bakwai ko takwas kafin su kammala karatu. Ya ce a karshe sai su kammala amma ba ilimin a kansu domin yawancin lokaci suna gida sanadiyar yajin aiki idan sun koma kuma sai su shiga jarabawa. To ta yaya irin wannan lamarin zai taimaki cigaban ilimi?

To amma ya yi kashedin kada malaman jami'a su daukesu a matsayin 'yan amshin shatan gwamnati. A'a a matsayinsu na iyaye ya kamata su nuna kukansu da damuwarsu da yadda abubuwa ke faruwa da suka shafi cigaban kasar. Kamata yayi malaman su daukesu a matsayin iyaye dake cike da damuwa domin 'ya'yansu da yadda jami'o'inmu ke tabarbarewa.

Ya kira malaman su janye yajin aikin ita kuma gwamnatin tarayya ta zauna da su domin samo bakin zaren matsalolinsu.

Sultan ya yi mamakin yadda yaje-yajen aiki suka kara dawowa jami'o'in Najeriya duk da namijin kokarin da suka yi a lokacin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.Ya ce da na yi zaton mun shawo kan wannan matsalar amma sai gashi mun koma gidan jiya. Don haka ya kira malaman da gwamnatin tarayya su yi hakuri, su kai zuciya nesa su zauna su tattauna matsalolinsu domin kawo karshen cecekuce da ya dabaibaye cigaban ilimi a Najeriya.

Murtala Faruk Sanyinna nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG