Abokiyar aiki Jummai Ali ta zanta da wasu mazauna jihar Yobe domin sanin musabbabin kafa wannan sabuwar dokar kwana biyu kacal da za'a gama azumi da kuma salla. Wadanda a ka zanta da su sun ce su basu san abun da ya faru ba har ya kai ga kafa irin wannan dokar hana fita dare da rana. Sai dai a matsayinsu na masu kiyaye doka kowa ya zauna a gidansa kamar yadda dokar ta tanada. Shugaban 'yan acaba ya ce ya kira duk ilahirin mutanesa ya kuma umurcesu su bi dokar domin a samu zaman lafiya.
Game da rayuwar yau da kullum mutane sun ce dokar ta shafi rayuwarsu. Mutane sun tagayyara domin abu ne ba'a kwana da shi ba amma aka tashi da shi. Yawancin mutane sai sun fita kafin su samu abun da zasu ci da iyalansu. Idan basu samu sun fita ba dare da rana yaya ke nan zasu rayu? Da aka ce kila an dauki matakin ne domin mahukuntan suna da hujja sai suka ce duk da hujjar ya kamata a duba rayuwar mutane tun da ba wani tallafi gwamnati ke bayarwa ba idan an kafa irin wannan dokar. Ana iya kiyaye tsaro ba tare da tauye hakin wani ba. Suna ganin kafa wannan dokar tamkar tauye hakin bil adama ne a jihar. Kamar yadda suka ce an zalunci jama'a da kafa dokar kodama an yi ne domin tabbatar da zaman lafiya. Kafin dokar sun ce an samu zaman lafiya fiye da da can kuma kawo yanzu basu ji wani abu mummuna ya faru a jihar ba.Lokacin dama abubuwa suka yi muni a jihar ba'a sa irin wannan doka ta hana fita dare da rana ba.
A tunanen jama'a duk wanda ya sa dokar bai yi tunanin mutane ba kuma bai dauki mutanen jihar wani abu ba. Kodayake sun yadda gwamnati ta dauki matakin tsaro amma ba da tauyewa talaka hakinsa ba kamar wannan dokar. Wani korafi kuma da mutane suka yi shi ne ba'a fada masu irin nasarorin da aka samu domin su samu kwarin gwiwa sai kwatsam a kakaba masu doka. Ya kamata kuma a rika gayawa mutane dalilin kafa irin wannan dokar.
Ga karin bayani.