A wata takarda da rundunar 'yansandan Kano ta fitar ta umurci duk masu zuwa masalacin idi da su guji rike kome a hannunsu inba darduma ba. Sun hana kowa rike kome zuwa idi. Takardar ta kara da cewa mutane su tuntubi hukumar idan sun ga idon da basu saba da shi ba ko kuma wani abu kamar jaka, gwangwani da dai makamantansu. Sanarwar da bukaci jama'a su cigaba da ba rundunar goyon bayan da suka saba bayarwa domin a tsare zaman lafiya.
Ita ma hukumar dake kula da sintirin motoci ta ce ta dauki duk matakan da suka kamata domin dakile duk wani hadarin mota lokacin bikin. Hukumar ta lura cewa yanzu hadarin mota ya koma cikin gari sabili da yadda masu hannu da shuni ke barin yara kanana suna tuka motoci da dan karen gudu a cikin gari. Jami'in hukumar ya ce tun ranar Litinin suka hada hannu da 'yansanda da sojoji da wasu jam'an kuma duk wani yaro da ya kama gudu da mota a cikin gari zasu kamashi su kuma hukunta shi ko dan wanene. Zasu cigaba da yin hakan har wajen kwana goma bayan salla.
Tuni dai hukumomi suka tsaurara matakan tsaro a ciki da kewayen Kano a shirin ko ta kwana da kuma tsare rayuka da ma dukiyoyin jama'a.
Mahmud Ibrahim Kwari nada karin bayani.