Sufeta Janar din Dr. Kayode Egbetokun ya ce cikin makonni biyar din da su ka gabata, zaratan 'yan sandan sun nuna su jajirtattu ne wajen tsare doka da oda ta hanyar tsarawa da aiwatar da farmaki akan miyagun iri.
Shugaban 'yan sandan ya ce rundunar ta katse hanzarin wasu gungun masu tafka miyagun laifuka inda aka cafke 'yan fashi da makami kimanin su 288, masu satar mutane don neman kudin fansa kuma 178.
'Yan sandan sun kuma cafke' yan ina da kisa guda 198 da karin wasu mutane sama da hamsin da ke rike da haramtattun makamai da ma yan kungiyoyin asiri sama da dari biyu.
Sufeto Janar din ya ce koda baya ga kwato bindigogi sama da dari da ashirin da harsasai 600 sun kuma ceto mutanen da ake garkuwa da su 71 daga hanun masu garkuwa da mutane da motocin sata kusan daei
Kazalika, Dr. Egbetokun ya nanata kudirin rundunar cewa za ta ci gaba da kwato makamai daga hannun jama' da aka mallaka ba bisa ka'ida ba, inda ya nemi duk wadanda ke rike da irin makaman da ya yi wa kansa kiyamullayli ya wanke kafa ya sadada caji ofis mafi kusa ya mika su salin-alin.
Dandalin Mu Tattauna