Tsare wadannan mutane da akayi ya kawo cikas ga tattaunawa tsakanin gwamnatin Salva Kiir da ‘yan tawa masu goyon bayan tsohon mataimakinsa Riek Machar.
A tattaunawa da yayi da sashen turanci na Muryar Amurka, kakakin shugaban kasa Ateny Wek Ateny yace daga yanzu ‘yan tawaye baza suyi amfani da wujjar tsare wadannan mutane da ake zargi da yunkurin juyin mulki domin kin hawa teburin shawarwari.
Shine kakaki Ateny yace "wannan batu ne mai matukar muhimmanci saboda mutane hudun da ake zargi da yunkurin juyin mulki, babu wanda zai yi amfani da su yanzu a matsayin hujjar kin hawa teburin shawarwari."
Gwamnatin kasar ta kame wadannan shuwagabannin siyasa ne bayan da shugaba Kirr a watan Decembar bara ya zargi Machar da kokarin juyin mulki.
Wannan kazafi kuwa, shine yayi sanadiyar fada tsakanin sojojin masu goyon bayan Kiir, da wadanda ke goyon bayan Machar.