Wani jami'in hukumar ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai suna Toby Lanzer ya ziyarci Bentiu babban birnin jihar Unity a jiya Alhamis. A wasu jerin sakonnin "twiter" da ya aike ya ce kusan bai ma ga farar hula ko guda ba a tsakiuyar garin, ya kuma ce shagunan da ke babbar kasuwar duk an yi wasosonsu kuma an lalata akasari.
Rahotannin da ke fitowa daga yankin na nuna cewa rundunonin sojin da ke biyayya ga Shugaba Salva Kiir na dannawa zuwa garin, wanda ya kasance karkashin ikon 'yan tawaye na tsawon makonni, wadanda ke biyayya ga abokin gaban Shugaban wato Riek Machar.
A halin da ake ciki kuma shirin tattauna zaman lafiya a kasar Ethiopea mai makwabtaka da ita ya cije, saboda gwamnati ta ke amincewa da bukatar 'yantwayen na sakin fursunonin siyasa 11.
Wani mai magana da yawun 'yan tawayen a birnin Addis Ababa ya yi amfani da tsaikon da aka samu a jiya Alhamis wajen zargin dakarun kasar Uganda da kai hari kan wuraren 'yan tawayen. To amma kasar Uganda ta ce sojojinta na Sudan ta Kudu ne don kawai su kare 'yan kasar Uganda da su ka makale.
A nasa martanin kuma shugaban tawagar gwamnatin Sudan wajen tattaunawar ya yi watsi da ikirarin 'yan tawayen na cewa Uganda ta kai masu hari ta sama da cewa mummar farfaganda ce kawai.