Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tallafin Ayyukan Jinkai A Sudan Ta Kudu


The White House
The White House

Shekarar 2021 na nuna alamun zata kasance mawuyaciya ga mutanen Sudan ta Kuda. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, kasar na fuskantar mummunar karancin abinci da ma rashin abinci mai gina jiki tun lokacin da ta samu ‘yancinta daga Sudan shekaru 10 da suka gabata.

Hakika, lokacin yunwa mai zuwa daga watan Mayu zuwa Yuli ana tsammanin zai zama mafi tsananin da ba a taba gani ba. Kimanin mutane miliyan 7.7 - kusan kashi biyu cikin uku na yawan al’ummar - za su buƙaci taimakon abinci, gami da kimanin yara miliyan 1.4 da ke fama da mummunan yunwa.

Bala'in yanayi na daga cikin matsalolin. Tasirin mummunar ambaliyar na kwanan nan, ya haɗe da annobar COVID-19. Amma yawancin matsalar mutane ne suka haifar da ita, sakamakon rashin zaman lafiya da ya haifar da yakin basasa na tsawon shekaru, rikice-rikicen tsakanin kabilu, fadan ‘yan siyasa, da ma cin hanci da rashawa.

Rikicin ya kara ta'azzara ne sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a shekarar da ta gabata, barnar farar dango, da kuma annobar COVID-19.

A tsakiyar watan Afrilu, Amurka ta sanar da cewa za ta isar da fiye da dala miliyan 95 don karin taimakon jin kai ga mutanen Sudan ta Kudu da ke fuskantar matsanancin karancin abinci da ke iya rikidewa ya zama mummunar yunwa a wasu yankuna na Sudan ta Kudu.

Wannan ya kawo jimillar taimakon agajin Amurka fiye da dala miliyan 482 kawo yanzu a cikin shekara ta 2021.

Da wadannan kudaden, gwamnatin Amurka za ta samar da mahimman ayyukan kiwon lafiyar jiki, kariya, mafaka, samun ingantaccen ruwan sha, da tsaftar muhalli kuma ba shakka, abinci mai gina jiki, ga wasu miliyoyin mutanen da abin ya shafa.

Mafi yawan abincin zai kasance Hukumar Kula da Ci Gaban Kasashen Duniya ta Amurka, ko USAID ce za ta saya daga manoman yankin Kudancin Sudan waɗanda suka sami damar girbin amfanin gonarsu a wannan lokacin. Ta wannan hanyar, USAID ke fatan karfafa samar da abinci a wannan shekara.

Wannan tallafi na Amurka za a fadada shi har ga mutanen da suka rasa muhallinsu, da kuma 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu a cikin al'ummomin da suka karbi bakuncinsu a Uganda, Sudan, Habasha, Kenya, da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Kasar Amurka ta fi kowace kasa bayar da agaji ga al’umar Kudancin Sudan. Taimakon jin kai ba zai warware masifar Sudan ta Kudu ba wanda dan Adam ne yayi sanadiyarta, amma yana da mahimmanci don kiyayewa da rayar da fararen hula da kuma rage wahala. Daga karshe, hanyar siyasa ita ce hanya daya tilo wacce zata kawo karshen wahalar da mutanen Sudan ta Kudu suke ciki.

XS
SM
MD
LG