Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Za Ta Binciki Yadda Aka Kashe Dala Miliyan 40 Kan COVID-19


Shugaban Kamaru, Paul Biya
Shugaban Kamaru, Paul Biya

Hukumomin Kamaru sun ba da umurnin kaddamar da bincike kan yadda aka sarrafa kudaden tallafin da fararen hula suka bayar a matsayin gudunmowa wandanda aka zuba su a wani asusu na musamman don yaki da cutar COVID-19 a kasar.

Umurnin na zuwa ne bayan da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka nuna matsin lamba kan a gudanar da binciken, inda suka yi zargin cewa an wawure dala miliyan 40 da aka tara na kudade da kayayyakin aiki da jama’a suka bayar a matsayin taimako.

Koken nasu ya samo asali ne bayan da kungiyoyin suka yi zargin cewa an sayar da buhun shinkafa dubu hudu wadanda asalinsu na tallafi ne da aka tanadawa wadanda suka kamu da cutar COVID-19.

Yadda wani ma'aikacin jinya ke shirin fara kula da masu COVID-19 a Kamaru
Yadda wani ma'aikacin jinya ke shirin fara kula da masu COVID-19 a Kamaru

Ko da yake, hukumomin kasar sun ce an sayi isasssun kayayyakin gwajin lafiyar jiki, sabulu, man kashe kwayoyin cuta, takunkumin rufe baki da hanci, magunguna tare da raba wadataccen ruwa a duk fadin kasar.

Shi dai Shugaba Paul Biya ya zuba dala miliyan 1.8 a asusun tallafin baya ga fararen hula, kamfanoni, ministoci da ‘yan majalisu da suka ba da tasu gudunmowar.

Kasar ta Kamaru har ila yau ta samu tallafi daga kasashen waje domin yaki da cutar ta COVID-19.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG