Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Tunisia Ya Nada Hichem a Matsayin Sabon Firai Minista


An Nada Ministan Cikin Gidan Tunisia Hichem Mechichi a Matsayin Sabon Firai Ministan Kasar
An Nada Ministan Cikin Gidan Tunisia Hichem Mechichi a Matsayin Sabon Firai Ministan Kasar

A ranar Asabar 25 ga watan Yuli Shugaban Tunisia Kais Saied ya nada Ministan cikin gidan kasar a matsayin sabon Firai Ministan da zai maye gurbin Elyes Fakhfakh, wanda ya yi murabus saboda zarge-zargen sabanin ra’ayi, a cewar fadar gwamnatin kasar.

Sabon Firai Minista Hichem Mechichi ya yi alkawarin daukar matakai akan bukace-bukacen harkokin zamantakewa da tattalin arziki da ke haddasa yawan zanga-zanga a kasar da ke arewacin nahiyar Afrika.

Mechichi, dan shekara 46, ya na da tsawon wata guda ya kafa gwamnatin da za ta samu nasara da rinjaye a kuri’ar kwarin gwiwa da majalisar dokokin za ta kada, ko kuma Shugaban zai soke majalisar dokokin ya sa a sake yin zabe.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG