Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Motar Safa Da Ke Jigilar Daliban Najeriya Ta Kama Da Wuta A Sudan


Mutane sun tsaya kusa da motocin safa yayin da fasinjoji da suka tsere daga Sudan suka isa tashar jirgin ruwa ta Argeen, bayan an kwashe su daga Khartoum zuwa birnin Abu Simbel, a saman kogin Nile a Aswan.
Mutane sun tsaya kusa da motocin safa yayin da fasinjoji da suka tsere daga Sudan suka isa tashar jirgin ruwa ta Argeen, bayan an kwashe su daga Khartoum zuwa birnin Abu Simbel, a saman kogin Nile a Aswan.

Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa babu wani fasinja da ya samu rauni bayan aukuwar hadarin.

Daya daga cikin motocin safa din da ke jigilar ‘yan Najeriya da suka makale daga Khartoum, babban birnin kasar Sudan, zuwa tashar jiragen ruwa ta Sudan wato Port Sudan, inda za’a dauke su zuwa kasar Saudiyya ta kama da wuta da sanyin safiyar ranar Litinin.

Motocin safa 26 ne dauke da ‘yan Najeriya da suka makale suka bar Al Razi da misalin karfe 12 na safiyar ranar Litinin zuwa Port Sudan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, daya daga cikin motocin safa din da ke jigilar dalibai ‘yan Najeriya kimanin 50 daga kasar Sudan mai lamba (Katsina 1) da ke kan hanyar zuwa Port Sudan a wani bangare na zagaye na biyu na Gwamnatin Tarayyar Najeriya na kwashe ‘yan kasar, ta samu matsala saboda tsananin zafi da daya daga cikin tayoyin motar ta yi.

Shugaban kungiyar Dattawan Najeriya da ke kasar Sudan, Dokta Hashim Idris Na’Allah, na daya daga cikin fasinjojin da ke cikin motar safa din, wadda ke dauke da dalibai 50 da suka hada da maza 49 da mace 1.

Wannan lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 2:30 na safe agogon Sudan.

Direban ya tsayar da motar safa din a kusa da wani shigen bincike na dakarun RSF, kafin tayar motar ta fashe wanda ya yi sanadin tashin gobara.

Sai dai dukkan fasinjojin sun tsira ba tare da wani rauni ba.

An raba 40 daga cikin fasinjojin 50 ga sauran motacin safa din da ke kwashe daliban, yayin da sauran fasinjojin suka kwana inda lamarin ya faru tare da direban a shingen binciken dakarun RSF.

“Daliban sun ce da gaske dakarun RSF sun yi iya kokarinsu wajen taimaka wa fasinjojin tare da ba su kofunan shayi da safe kafin su tafi,” in ji Sani Aliyu da ke Sudan.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa tun daga lokacin suka ci gaba da tafiya zuwa Port Sudan.

Fiye da ‘yan Najeriya 1,000 ne aka kwashe su ta hanyar Port Sudan sakamakon matsalolin da aka fuskanta wajen wadanda aka kwashe na farko a kan iyakokin kasar Masar.

‘Yan Najeriya da suka makale sun shafe kwanaki biyar a kan iyakokin kasar yayin da jami’an Masar suka hana su shiga kasar, inda tuni jirage ke jiran kwashe su zuwa Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG