Kwale-kwalen dogaran gabar teku sun ceci mutane daga jiragen ruwan da suka cika fiye da kima a zirin Gibralta da kuma Tekun Albonan, wadannan wurare mafi kusa tsakanin kasar Spain da gabatar tekun arewacin nahiyar Afrika.
Kungiyar lura da kaurar jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a bana kurum fiye da mutane dubu goma sha takwas daga arewacin Afrika suka isa kasar Spain.
Kasar Spain ta maye gurbin kasar Italiya a zaman kasar da bakin haure daga nahiyar Afrika da kasashen Syria da Afghanistan da kuma wasu wurare da suke kokarin arcewa daga yaki da talauci, suke son zuwa domin samun rayuwa mai inganci.
Kasar Italiya wadda take fama da yawan bakin haure karkashin wata yarjejeniyar da ta kulla da kasar Libya, yanzu ta fara maida su bakin hauren kasashensu maimakon neman musu mafaka.
Facebook Forum