Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da wata takardar bayani, inda ya ke bayyana cewa ya yi matukar kaduwa da yadda tashin hankali ke kara muni a Gaza da kuma kudancin Isira’ila.
“Ina kira ga Hamas da sauran mayakan Falasdinawa da kawo karshen cilla rokoki da sauran take-taken takala a tsawon kan iya,” a cewar Antonio Guterres a jiya Asabar. Ya kara da cewa, “Dole ita kuma Isira’ila ta kai zuciya nesa don kauce ma dada dagula lamarin.”
Guterres ya cigaba da gargadin cewa muddun al’amarin ya cigaba da ta’azzara, rayukan jama da dama za su kasance cikin hadarin gaske, wanda hakan zai kuma dada tsananin matsalar jinkai a yankin na Gaza; karshenta kuma hakan zai kawo dusashewar goyon bayan hukumar Falasdinu a yankin.
Facebook Forum