Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia Ta Kama Manyan Makamai


Dakarun kasar Somalia suna binciken mayakan Al shebab, Yuni, 2, 2012.
Dakarun kasar Somalia suna binciken mayakan Al shebab, Yuni, 2, 2012.

An kama manyan makamai a kasar Somalia, kwanaki kadan bayan da hukumomin kasar suka nemi a dage masu takunkumin sayen makamai da aka kakabawa kasar, domin su yaki kungiyar Al shebab.

Hukumomin a yankin Puntland na kasar Somalia mai cin kwarya-kwaryan gashin kansa, sun ce sun kama wani jirgin ruwa makare da makamai, kamar yadda suka bayyanawa Muryar Amurka.

Mukaddashin ‘yan sandan yankin, Mohammed Mohamud Hassan ya ce, makaman sun hada da manyan bindigogi nau’in AK47 da bindigar kakkabo jiragen sama da kuma harsashai.

A cewar shi, sun kama jirgin ne yayin da yake kokarin tserewa a kusa da yankin gabar ruwan Mareero da ke da tazarar kilomita tara daga gabashin yankin Bosaso, yanki mafi girma da ke dauke da tashar jiragen ruwa da kuma yawan hadahadar kasuwanci.

Yayin da suka baje makaman a gaban manema labarai, hukumomin kasar sun ce suna gudanar da bincike domin gano ko na wane ne makaman, sannan kuma ina aka dosa da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG