Kafar yada laraban kasar ta ruwaito cewa harin ya daidaita na’urar harba rokoki da dama.
A cewar rahotanni, hare-haren da dakarun kasa suka kai, ya kashe mayakan na IS 34 yayin da hare-haren jirgi mara matuki ya halaka wasu 29.
Martanin da dakarun kasar ta Turkiyya suka kai, ya auku ne bayan da aka harba wasu rokoki akan birnin Kilis da ke Turkiya a kusa da arewacin kan iyakar Syria, harin da ya raunata mutane takwas.
A wani lamari na dabna kuma, a ranar Lahadi wata mota shake da bama-bamai ita ma ta fashe a kofar ofishin ‘yan sanda da ke Gaziantep a kusa da kan iyakar Syria.
Harin ya kashe ‘yan sanda biyu sannan ya raunata wasu 22.
Amma ya zuwa yanzua babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari.