A siyasar Amurka, zaman dar-dar tayi tsanani a harabar wani O'tel a jihar California, inda Donald Trump, yayi jawabi ga wani taron 'yan jam'iyyar Republican.
Trump, ya yada zango a kwazazzabun Silicon, da galibin mazauna yankin masu sassaucin ra'yi ne jiya jumma'a, kwana daya bayan da tarzoma ta barke a wani gangamin yakin neman zabensa a karamar hukumar Orange, inda galibin mazauna yankin su kuma masu ra'ayin mazan jiya ne.
A jiyan, fiyeda masu zanga-zanga su dari uku ne suka cika harabar O'tel dake kusa da babbar tashar jirgin sama dake San Francisco, al'amari da ya tilastawa Trump, kusan yin rarrafe ta karkashin shinge, domin ya shiga O'tel din. Trump, ya gayawa mahalarta taron cewa, "wannan shine shiga wuri mafi tsanani da ya taba yi,". Ji nake kamar ina tsallakawa ne ta kan iyaka," inji Trump, yana misali ne da yadda bakin haure wadanda galibi matakan tsaro ke tilastawa yin haka domin su shiga Amurka daga kan iyakarta dake kudanci.
Masu zanga-zangar, wasu sun rurrufe fuskokinsu da mayani, suna kuma dauke da tutar kasar Mexico, da alamomi na nuna rashin amincewa da shirin Trump, wanda ya janyo kace-nace, kan batun gina katanga kan iyakar Amurka da Mexico, domin hana bakin haure shigowa. Sunyi kokarin su kutsa cikin O'tel din, amma 'Yansanda suka tare su.
Zaben fidda gwani da za'a yi nan kusa shine a jihar Indiana, jiharta galibin jama'arta, masu ra'ayin rikau ne.
Idan Trump ya sami nasara a jihar, hakan ba wai a hukumance ya sami nasarar zama dan takara ba, amma zai bashi babbar tazara, a dai dai lokacinda za'a shiga zabe a jihohi tara na karshe, da za'a yi a farko farkon watan Yuni.