Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam ya tashi gaban hedkwatar 'yansanda Gaziantep dake Turkiya


Gangar motar da ta tarwatse da bam a Geziantep
Gangar motar da ta tarwatse da bam a Geziantep

Bam ya tarwatsa wata mota gaban hekwatar rundunar 'yansandan kudu maso gabashin birnin Gaziantep dale kasar Turkiya inda ya kashe akalla 'yansanda biyu ya kuma jikata kijata wasu mutane 22 kamar yadda gwamnan yakin ya sanar.

Kafofin labaran kasar Turkiya sun ambato gwamnan yankin Ali Yerlikaya yana cewa yawancin wadanda suka jikata a harin jiya Lahadi 'yansanda ne.

Wani bidiyo da wata kafar labari mai zaman kanta ta nuna a gidan talibijan na NTV ya nuna irin yamutsi da ya auku bayan harin a gaban gini 'yansandan yayinda da masu wucewa ke kallon baraguzan gilashi da bangon da ya ruguje. Haka kuma an ga motocin asibitoci masu kawashe gawa ko wadanda suka jikata suna jigilar mutane..

Gaziantep shi ne birni mafi girma na shida a kasar Turkiya. Yana da mutane kimanin miliyan daya da rabi. Yana da tazarar kilimita 55 daga inda kungiyar ISIS ke da iko akan iyaka da kasar Syria. Birnin ne ya zama tamkar mafakar 'yan gudun hijira dake arcewa daga rikicin Syria.

Kodayake babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin amma 'yan ta'ada sun riga sun kai hari makamancin wannan har sau biyu a babban birnin kasar Istanbul cikin wannan shekarar.

Wurin da bam ya tashi a Gaziantep, Turkiya
Wurin da bam ya tashi a Gaziantep, Turkiya

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG