Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NajeriyaTa Bada Labarin Sakin Malaman Jami'ar Maiduguri Da Boko Haram Tayi Garkuwa Dasu.


Shugaba Buhari yake duba faretin soja a Maiduguri bara, lokacinda ya ziyarci jahar a karon farko tunda ya hau mulki.
Shugaba Buhari yake duba faretin soja a Maiduguri bara, lokacinda ya ziyarci jahar a karon farko tunda ya hau mulki.

Sanarwar hakan tana kunshe ne a cikin wata sanarwa daga fadar shugaban kasa da kakakin sa Garba Shehu ya sanya hanu akai.

Sanarwar tace, hukumar 'Yansanda na farin kaya, Asabar din nan ta yiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayani, kan sakin malaman jami'ar Maiduguri su uku, wadanda kungiyar Boko Haram ta sace su a bara .

Haka nan kungiyar Boko ta saki wasu mata su 10, wadanda mayakan kungiyar suka sace su, bayan da suka yiwa jerin gwanon motocin su kwanton bauna akan hanyar Damboa, kusa da Maiduguri.

Sanarwar tace sakin nasu ya biyo bayan shawarwari, kamar yadda shugaban kasa ya bada umarni a yi, inda kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross ta shiga tsakani.

Kamar yadda bayanan da hukumar ta 'Yansandan ciki ta baiwa shugaban kasa,, duka mutanen 13 suna hanun hukumar, kuma yanzu haka suna kan hanyar zuwa Abuja, tareda taimakon hukumomin sojan Najeriya na kasa dana sama.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:14 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG