Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankar Sojoji Ta Take, Ta Murkushe Motar Yaki Ta 'Yan Boko Haram


Motar Boko Haram Da Tankar Sojoji Ta Murkushe
Motar Boko Haram Da Tankar Sojoji Ta Murkushe

Wannan ya faru a lokacin da sojoji suka yi kwanton-bauna ma 'yan Boko Haram da suka gudo daga wani yankin dajin Sambisa a Goniri dake yankin karamar hukumar Gujba a Jihar Yobe.

Sojojin dake aiki karkashin shirin Operation lafiya Dole a Jihar Yobe, sun yi kwanton-bauna ma wasu 'yan Boko Haram da suka yi kokarin gudu daga cikin wani yanki na dajin Sambisa, inda ake kai musu farmaki.

A wannan lamarin da ya faru ranar jumma'a, sojojin sun buya suka tare wata hanya da 'yan Boko Haram suka biyo dauke da wata motar da suka sanya bama-bamai a ciki, wadda wata tankar yaki ta sojoji ta bi ta kanta ta lalata kafin ta sami kaiwa ga sojojin da suka yi kwanton baunar.

Mukaddashin kakakin Birged ta 27 ta sojojin dake yaki da Boko Haram, Manjo Nureni Alimi, ya fada cikin wata sanarwa cewa, a lokacin da 'yan Boko haram suka fada cikin wannan kwanton bauna da aka yi musu a Goniri, da misalin karfe 6 da minti 20 na maraicen Jumma'a, sai suka fara bude wuta ta ko ina, har suka ji rauni ma sojoji guda biyu.

Kakakin yace sojojin sun kashe 'yan Boko Haram da dama, inda a bayan wannan mota, suka kwace wata bindigar harbo jiragen sama, da kwanson harsasai, da bindiga kirar AK-47 da wasu kayayyakin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG